IQNA

Matashi Dan Kasar Masar Mai Fasahar Rubutun Kur’ani

22:58 - December 15, 2020
Lambar Labari: 3485461
Tehran (IQNA) wani matashi dan kasar Masar mai fasahar rubutu ya rubuta cikakken kur’ani mai tsarki a kan takarda.

Shafin jaridar Aldastur ta kasar Masar ya bayar da rahoton cewa, matashin mai suna Muhammad Hussain mai fasahar rubutu ya rubuta cikakken kwafin kur’ani mai tsarki a kan takarda, tare da kiyaye dukkanin ka’idoji na rubutu.

Rahoton ya ce Muhammad Hussain dan shekaru 20 da haihuwa, ya kasance mai matukar sha’war rubutun kur’ani mai tsarki tun yana karami, kuma yana yin rubutun lokaci zuwa lokaci domin sha’awa.

Amma daga bisani sakamakon karfin gwiwar da yake ya samu daga mahaifansa, da kuma malamansa  amakaransa, saboda yadda suka fahimci yana da himma a wannan bangare, ya ci gaba da kara bayar da himma matuka.

Ya ce mahaifinsa ya rasu tun lokacin yana shekaru 8 da hahihuwa, amma wannan bai karya masa gwiwa ba wajen ci gaba da koyon rubutun, domin kuwa babban burinsa shi ne ya ga cewa ya rubuta kur’ani daga farko har karshe.

Haka nan kuma ya bayyana cewa yana godiya ga Allah madaukakin sarki da ya ba shi damar rubuta cikakken kwafin kur’ani mai tsarki, wanda shi ne babban burinsa na rayuwa.

 

3940987

 

Abubuwan Da Ya Shafa: rubuta cikakken kwafin kur’ani
captcha