Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kwarya-kwaryan cin gishin kai ta Falastinawa ta sanar da cewa, zaman da babban zauren Majalisar dinkin duniya ya gudanar, ya nuna amincewa da hakkin Falastinawa na kafa kasa mai cin gishin kanta.
Ministan harkokin wajen gwamnatin Falastinu Riyad Maliki ya bayyana cewa, wannan kuduri ya kara tabbatar da cewa al’ummomin duniya ba su tare da mamayar da Isra’ila take yi wa Falastinu, inda suke goyon bayan kafa kasar Falastinu mai cin gishin kanta.
Kasashe 168 ne suka amince da wannan kudiri, yayin da 5 kuma suka ki amincewa da shi, sai kuma 10 suka ki kada kuri’ar amincewa ko rashin amincewa da kudirin.
Babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince da kudurori 6 dukkaninsu da suke nuna goyon baya da amincewa kan kafa kasar Falastinu mai cin gashin kanta, amma kudurorin ba su da hurumin tilasta yin aiki da su.