IQNA

23:52 - December 22, 2020
Lambar Labari: 3485482
Tehran (IQNA) musulmi da dama a duniya sun shiga cikin halin rudu kan halascin allurar rigakafin cutar corona, bisa zargin cewa an yi amfani da wani bangaren alade a cikinta.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, tun bayan da wasu bayanai suka bayyana kan cewa an yi amfani da wani bangaren alade wajen hada rigakafin cutar corona, musulmi da dama a duniya sun shiga cikin rudu kan halascin wannan allura.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kamfanonin magunguna na wasu kasashe, da suka hada da Amurka da kuma Rasha gami da China da Jamus suka sanar da samun rigakafin cutar ta corona, kuma tuni aka fara yi wa mutane wannan riga kafi.

To sai bayan samun bayanai kan cewa akwai wani abin da aka dauka daga jikin alade wajen hada wannan rigakafi, hakan ya tayar da hankulan musulmi a duniya, kan halasin allurer.

Dr. Salman Waqar wani likita ne musulmi dan kasar Burtaniya ya bayyana cewa, akwai yiwuwar wasu sanadaran alade da ake sakawa a cikin allurai na rigafi su karu a nan gaba, kasantuwar wasu masana na cewa haka ne zai sanya rigakafin ta jima tana bayar da kariya ga jikin dan adam.

Wani malamin ilimin likitanci a jami’ar Sydney a kasar Australia mai suna Harun Rashid wanda shi ma musulmi ne, ya bayyana cewa, bisa la’akari da matsala da illar corona wadda take cutar da kowa a duniya, wasu malaman musulmi sun halasta yin amfani da rigafin cutar corona ko da kuwa an yi amfani da wasu sanadarai da suke da alaka da alade, wannan kuwa tana a matsayin fatawa ta halin lalura kamar yadda ya ambata.

3942559

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: