IQNA

Abu Mahdi Almuhandis A Lokacin Da Yake Ziyartar Mabiya Addinai Marassa Rinjaye A Iraki

21:41 - December 28, 2020
Lambar Labari: 3485502
Tehran (IQNA) kafin kisan gillar da Amurka da ta yi masa, Abu Mahdi yana ziyartar wasu mabiya addinai marassa rinjaye a Iraki domin jin halin da suke ciki.

Abu Mahdi Almuhandis mataimakin babban kwamandan dakarun Hashd Al-shaabi a Iraki a kisan gillar da Amurka da ta yi masa a 2019, ya ziyarci wasu mabiya addinai marassa rinjaye a Iraki, domin jin yanayin da suke ciki ta fuskar tsaro a cikin yankin Sahal a lardin Nainawa.

A yayin ganawarsa da wasu jagororin mabiya addinin kirista, Almuhandis ya sheda musu cewa, dakarun Hashd ba za su kasa a gwiwa wajen kare dukkanin yankunan Iraki ba, kamar yadda wuraren ibada na musulmi da na wadanda ba musulmi ba, za su zama cikin wuraren da za su rika ba su kariya daga hare-haren ‘yan ta’adda.

Abu mahdi Almuhandis dai ya kasance mai bayar da kulawa ta musamman ga al’ummomi marassa rinjaye a kasar Iraki.

Amurka ta kashe Abu mahdi Almuhandis ne tare da babban kwamandan dakarun Iran Qassem Sulaimani a farkon wanann shekara mai karewa.

3943634

 

 

 

 

 

captcha