IQNA

22:56 - December 31, 2020
Lambar Labari: 3485510
Tehran (IQNA) Gwamnatin San’a a kasar Yemen ta bayyana cewa, harin da aka kai a Aden sakamako ne na rikicin cikin gida tsakanin ‘yan mamaya da ‘yan korensu.

A cikin bayanin da gwamnatin San’a ta fitar ta bayyana cewa, wannan hari ya auku ne sakamakon irin matsanancin sabanin da ke tsakanin ‘yan mamaya da suke hankoron mamaye kasar Yemen, da kuma wasu ‘yan kasar da suke mara musu baya saboda abin duniya.

Harin dai ya auku ne a lokacin da tawagar gwamnatin Hadi Mansur mai matsugunni a kasar Saudiyya ta iso birnin Aden da ke kudancin Yemen, inda isowar jirgin da ke dauke da su ke da wuya, sai manyan bama-bamai uku suka tarwatse a wurin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 20 wasu da dama kuma suka jikkata.

Gwamnatin Hadi Mansur ta tuhumi kungiyar Ansarullah ko kuma Alhuthi da kai harin, amma kungiyar ta mayar da martani da cewa, su dai nemi wadanda suka kai harin yaka junansu.

Kakakin gwamnatin San’a Shami Daifullah ya bayyana cewa, musayar wuta da aka samu tsakanin jami’an tsaron gwamnatin Hadi da wadanda suke tare da su a filin jirgin, ya kara tabbatar da cewa rikcin na cikin gida ne a  tsakaninsu.

Hadi Mansur da ya tsere daga Yemen ne zuwa birnin Riyad na Saudiyya, inda ya kafa gwamnati a can da ke da matsugunni a cikin manyan otel-otel na birnin Riyad.

3944541

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: