IQNA

Paparoma Ya Bukaci A Kawo Karshen Yaki Kan Kasar Yemen

23:21 - January 02, 2021
Lambar Labari: 3485518
Tehran (IQNA) Jagoran mabiya addinin kirista ‘yan darikar Katolika Paparoma Francis, ya nuna matukar damuwa kan halin da al’ummar Yemen suke ciki.

A cikin bayaninsa na sabuwar shekara, Jagoran mabiya addinin kirista ‘yan darikar Katolika Paparoma Francis ya bayyana cewa, yana cikin damuwa da bakin ciki matuka dangane da mawuyacin halin da aka jefa al’ummar kasar Yemen tsawon shekaru shifa a jere.

Ya ce bai kamata mu manta da halin da mata da kanan yara da tsoffi da fararen hula suke ciki a kasar Yemen ba.

Ya kara da cewa, yara da dama an haramta musu zuwa makaranta, mutane da dama, ba su ji ba su gani ba sun rasa rayuwarsu, yunwa tana kassara mutane mata da kanan yara, ya ce yana fatan shekara ta 2021 ta zama shekarar sulhu da samun zaman lafiya da kawo karshen yaki a kan kasar Yemen.

Ko a cikin wannan makon nan, manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kan rikicin Yemen Martin Griffiths, sai da ya jaddada wajabcin kawo karshen yakin kasar Yemen, tare da bayyana fatan shekara ta 2021 ta zama shekarar karshe ta yakin da ake yi a kasar.

Tun bayan da gwamnatin Saudiyya ta fara kaddamar da hari kan al’ummar Yemen shekaru 6 da suka gabata, ya zuwa yanzu dubban fararen hula mata da kananan yara da tsoffi ne suka rasa rayukansu, wasu dubbai kuma suka jikkata, yayin da wasu miliyoyi kuma suka zama ‘yan gudun hijira.

 

3944839

 

captcha