
Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa gwamnatin kasar Habasha ta bayar da sanarwar cewa, za ta sake gyara tsohon masallacin Najjashi, wanda daya ne daga cikin masallatan musulmi mafi dadewa a tarihi.
Wannan masallaci dai an gina shi ne a yankin arewa maso yammacin kasar Habasha a lokacin da wasu daga cikin sahabban manzon Allah (SAW) karkashin jagorancin Ja'afar Ibn Abi Talib, dan Ammin manzon Allah wato Abu Talib, suka yi hijira daga Makka zuwa Habasha, inda sarkin Habasha na lokaci wato sarki Najjashi ya karbe su kuma ya ba su kariya daga cutarwar muhsrikan Makka.
A halin yanzu yankin da aka gina masallacin yana da tazarar kilo mita 790 daga birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar ta Habasha, inda a nan aka bizne gawawwakin sahabbai 15 daga cikin sahabban farko da suka hijira zuwa Habasha.
Wasu na bayyana wannan masallaci a matsayin wurin ibadar musulmi na biyu bayan bayyanar addinin muslunci, inda a nan sahabbai na farko da suka yi hijira suka gina masallaci domin yin ibada.
A cikin watannain da suka gabata ne dai aka rusa wani bangaren masallacin, sakamakon arangamar da aka yi tsakanin dakarun gwamnati da kuma ‘yan arewacin Tigray na kasar.
Yanzu haka dai gwamnatin Habasha tura jami’ai domin duba yanayin masallacin da kuma kiyasta kudaden da za a kashe domin sake gyara shi.