IQNA

Amurka Ta Kakaba Wa Babban Kwamanda Hashd Al-shaabi Na Kasar Iraki Takunkumi

22:16 - January 09, 2021
Lambar Labari: 3485538
Tehran (IQNA) Dakarun sa kai na Hashd Al-shaabi a Iraki sun mayar da kakkausan martani kan takunkuman da Amurka ta kakaba wa Faleh Fayyad.

A cikin wani bayani wanda bangaren yada labarai na rundunar Hashd Al-shaabi ya fitar, ya bayyana takunkumin Amurka a kan Faleh Fayyad da cewa abin alfahari ne a gare shi da ma dukkanin dakarun Hashd Al-shaabi.

Bayanin ya ce, wannan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka a kan mutumin da ya kasance a sahun gaba wajen yakar ‘yan ta’addan Daesh a Iraki, tare da fatattakarsu da karya lagonsu, ya kara fito da komai a fili kan cewa, Amurka da Daesh da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi duk abu daya ne, domin kuwa babbar manufarsu ita ce rusa kasashen musulmi da kuma bata sunan addinin muslunci a idon duniya.

A jiya ne gwamnatin Trump ta sanar da cewa ta saka babban kwamandan dakarun Hashd Al-shaabi na kasar Iraki Faleh Fayyad a cikin jerin wadanda ta kakaba wa takunkumi.

Tun kafin wannan lokacin dai Fayyad ya tsaya kai da fata akan cewa dole ne Amurka ta fitar da dukkanin sojojinta da suka rage a cikin Iraki, bayan da majalisar dokokin kasar ta fitar da wani kudiri kan hakan, inda ya jaddada cewa rashin ficewar dakarun Amurka daga Iraki, yana a matsayin tozarta majalisar dokokin kasar ne wadda take wakiltar dukkanin al’ummar Iraki.

3946445

 

 

captcha