IQNA

Sudan: Jama’a Na Bayar Da Himma Wajen Halartar Manyan Tarukan Tilawar Kur’ani A Masallatai

22:41 - January 09, 2021
Lambar Labari: 3485540
Tehran (IQNA) dubban jama’a suna halartar tarukan karatun kur’ani mai tsarki a masallatai.

Shafin yada labarai na Nilain ya bayar da rahoton cewa, dubban jama’a suna halartar tarukan karatun kur’ani mai tsarki a masallatai a birnin Khartum da sauran birane na kasar, wanda daya ne daga cikin dadaddun al’adu na mutanen kasar.

Ahmad Ali Abdulrahman shi ne mai kula da masallacin Abdulrahman Bin Auf a birnin Khartum ya bayyana cewa, sun jima suna gudanar da irin wadannan taruka a masallatai, domin samun albarkacin kur’ani da kuma lada mai yawa da take tattare da hakan.

Ya ce wani babban dan kasuwa ne mai suna Mahmud Muhammad Mahmud ya dauki nauyin gudanar da irin wannan taro na karatun kur’ani a wannan masallaci, inda aka tanadi abinci da abin sha ga dukkanin mahalrta wurin, wanda adadinsu yana da yawa.

Bisa ga abin da aka saba dai akan gayyaci makaranka masu kyakkyawan sauti na karatun kur’ani domin su gabatar da karatu a irin wannan taro, yayin da sauran jama’a da suke wurin suna zaune suna sauraro.

3946499

 

captcha