IQNA

Dare Na Biyu Na Zaman Juyayin Shahadar Fatima Zahra (AS)

23:17 - January 15, 2021
Lambar Labari: 3485556
Tehran (IQNA) an gudanar da zama a daren na biyu na juyayin shahadar Sayyida Fatima Zahra (AS) a Husainiyar Imam Khomeni.

A ci gaba da zaman juyin zagayowar lokacin shahadar Sayyida Fatima Zahra (AS) an gudanar da zama a dare na biyu tare da halartar jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

A yayin zaman an gabatar da jabi kan matsayin Sayyida Zahra da kuma yadda ta zama abin koyi ga dukkanin bil adama, wajen kyawawan dabi’unta, da kaskantar da kai da ibada ga Allah madaukakin sarki, da kuma ambaton Allah a cikin dukkanin lokutan rayuwarta.

3947886

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :