IQNA

Shirin Ayyukan Kur’ani Ta Hanyar Yanar Gizo Ya Samu Karbuwa A Tsakanin Mutanen Morocco

22:46 - January 24, 2021
Lambar Labari: 3485583
Tehran (IQNA) shirin ayyukan kur’ani ta hanyar yanar yanar gizo ya samu karbuwa  a tsakanin mutanen kasar Morocco.

Kafofin yada labarai a kasar Morocco sun bayar da rahotannin cewa, shin da aka gabatar da shi na ayyukan kur’ani ta hanyar yanar gizo ya samu karbuwa  a tsakanin mutanen kasar, sakamakon dakatar da irin wadannan shirye-shirye a masallatai da cibiyoyin kur’ani a kasar.

Hassan Bin Ibrahim ya shugaban kwamitin ayyukan kur’ani na Sukhairat ya bayyana cewa, an kirkiro shirin ne domin tabbatar da cewa an ci gaba da abin da ake yi tsawon shekaru a kasar, duk kuwa da cewa a wannan karon yadda ake gudanar da tsarin ya banbanta.

A lokutan baya jama’a suna taruwa a masallatai da cibiyoyin ilimin addinin domin daukar ilmomi da suka shafi kur’ani, da hakan ya hada da tilawa da sanin kaidoji da hukunce-hukuncen karatu na tajwidi, da ma wasu ilmomi na kur’ani mai tsarki.

Tun bayan bullar cutar corona aka dakatar da wannan shiri a fadin kasar, domin kaucewa daukar cutar ko kuma yada ta a tsakanin mutane, inda aka kirkiro manhaja da za a iya saukewa a wayoyi ko na’urorin kwamfuta, inda za a iya shiga cikin shirin kai, tare da koyon abubuwan da ake gabatarwa.

3949486

 

 

 

 

captcha