IQNA

​An Gudanar Da Taruka Da Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Al’ummar Yemen A Kasashen Duniya

22:28 - January 25, 2021
Lambar Labari: 3485587
Tehran (IQNA) A yau an gudanar da gangamin nuna goyon baya ga al’ummar kasar Yemen marassa kariya da ke fusakantar kisan kiyashi daga kawancen Saudiyya.​

Shafin yada labarai na 26 September ya bayar da rahoton cewa, a yau an gudanar da gangami gami da taruka na nuna goyon baya ga al’ummar kasar Yemen marassa kariya da ke fusakantar kisan kiyashi daga kawancen Saudiyya tsawon shekaru shida.

Rahoton ya kara da cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama daga kasashe 17 ne suka fitar da bayani na hadin gwiwa domin kiran al’ummomin duniya masu sauran lamiri, da su mike su nuna bacin ransu kan kisan da ake yi wa al’ummar Yemen babu gaira ba sabar.

Su ma a nasa bangaren Al’ummar kasar ta Yemen sun bayyana cewar ta’addanci na hakika shi ne abin da kawancen Amurka-Saudiyya suke aikatawa a kan al’ummar ƙasar Yemen na killace su da hana su dukkanin abubuwan da suke buƙata wajen gudanar da rayuwarsu.

An gudanar da gangamin ne a yau a birnin Sana’ don amsa kiran wadannan ƙungiyoyi da suka yi na gudanar da wannan gangami a masayin ‘Ranar Duniya Don Goyon Bayan Al’ummar Yemen’ sun kuma mayar da martani ga matakin da Amurka ta ɗauka na sanya ƙungiyar Ansarullah ta Yemen ɗin cikin ƙungiyoyin ta’addanci, tare da bayyana bin da Saudiyya da Amurka suke yin a kisan al’ummar Yemen shi ne ta’addanci.

3949509

 

captcha