IQNA

Ansarullah Ta Yi Maraba Da Matakin Gwamnatin Italiya Na Dakatar Da Sayar Wa Gwamnatin Saudiyya Da Makamai

23:09 - January 31, 2021
Lambar Labari: 3485608
Tehran (IQNA) Kungiyar Ansarullah ta Yemen, ta yi maraba da matakin kasar Italiya, na soke sayar wa da kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Laraba makamman yaki.

Kakakin kungiyar Ansarullah da aka fi sani da Al-huthi, Mohammed Abdul-Salam, ya wallafa a shafinsa na twitter cewa wannan mataki ne mai kyau kuma zai taimaka wajen karfafa zaman lafiya da kuma kare rayukan fararen hula a kasar ta Yemen da yakin tsawon shekaru ya daidaita.

A jiya Juma’a ne dai ministan harkokin wajen kasar Italiya, Luigi Di Maio, ya sanar ecwa kasarsa ta soke shirin mikawa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa makamai masu linzami da bama-bamai, wanda kasar ta dauki wannan matakin ne domin mutunta hakkin dan adam.

Tuni wasu kungiyoyin masu rajin tabbatar da zaman lafiya a Italiya su ma sukayi maraba da matakin, wanda suka ce ya hana mika wa kasashen Saudiyyar da hadaddiyar daular larabawa, bama bamai kimanin 12,700.

Dama dai kafin hakan sabon shugaban Amurka Joe Biden, ya sanar da irin wannan matakin na dakatar da shirin sayarwa kasashen biyu makamman yaki.

 

3950835

 

captcha