A ci gaba da aiwatar da shirin tattaunawa tsakanin addinai na duniya, a karon farko ana shirin gudanar da taron ranar ‘yan adamtaka tsakanin ‘yan adam ta duniya a kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar manyan malaman musulmi da kuma Paparoma Francis.
Tun lokacin da Paparoma ya yi tafiya zuwa kasar hadaddiyar daular larabawa a ranar 4 ga watan Fabrairun shekara ta 2019, tare da shekhul Azahar, aka rabbata hannu kan yarjeneiyar tattaunawa tsakanin addinai musamman kiristanci da musulmi a mataki na kasa da kasa.
Wannan taro dai zai samu halartar manyan malaman addini daga kasashen duniya da suka hada da Ahamd Tayyib babban malamin cibiyar Azhar, kamar yadda kuma wasu daga cikin masana daga sassa na duniya za su halarci, inda taron zai gudana birnin Abu Dhabi.
A ranar 21 ga watan Disamban 2020 babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince da daftarin kudiri na sanya ranar 4 ga kowane watan Fabrairu ta zama ranar ranar ‘yan adamtaka tsakanin ‘yan adam ta duniya, wanda kuma wannan shi ne karon farko da za a fara gudanar da taron.
Tun a cikin shekara ta 1964 marigayi Paparoma John Paul ya kafa wani kwamitia fadar Vatican domin shirya tataunawa tsakanin addinai.