IQNA

22:49 - February 08, 2021
Lambar Labari: 3485630
Tehran () jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya amince da yin afuwa ga wasu fursunoni da kuma sassauta hukunci a kan wasu.

A cikin wani bayani da shafin ofishin jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya fitar, an bayyana cewa jagoran ya amince da yin afuwa ga wasu fursunoni da kuma sassauci ga wasu, wadanda jimillar adadinu ya kai dubu 3 da 840.

Alkalin alkalan kasar ta Iran ne ya mika wannan bukata ga jagoran juyin, wanda a kowace shekara lokuta na musamman a kan aike da irin wannan bukata.

A wannan karon salbarkacin zagayowar lokacin cikar shekaru arba'in da biyu da samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar ta Iran, alkalin alkalai ya bukaci irin wannan alfarma.

3952838

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: