IQNA

Zaman Taro Kan Matsayin Sayyida Fatima Zahra (AS)

22:40 - February 10, 2021
Lambar Labari: 3485639
Tehran (IQNA) an gudanar da wani zaman taro kan matsayin Sayyida Fatima Zahra amincin Allah ya tabbata a gar eta.

A cikin rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, a yau an gudanar da wani zaman taro wanda ya yi dubi kan matsayin shugabar matan duniya diyar ma’aiki kuma mafi soyuwar dukkanin halittu a wurinsa, Fatima Zahra (AS).

Wannan taro dai ya samu halartar masana da masu bincike kan lamurran da suka shafi tarihin Sayyida Fatima Zahra (AS) wanda ya hada dukkanin bangarori na mabiya mazhabar ahlul bait da kuma mabiya mazhabobin sunnah a cikin kasar Iran.

Haka nan kuma a taron an bijiro da abubuwa da dama da suka tabbata a cikin tarihi wadanda dukkanin bangarorin biyu sun ruwaito su a cikin ruwayoyinsu dangane da matsayinta madaukaki.

Mafi yawan wadanda suka gabatar da bayanai a taron dai masana ne mata da kuam malaman jami’a a cikin da wajen kasar Iran, wadanda suke gudanar da bicike kan ilimin tarihi musamman na addinin muslunci.

A shekarun baya dai ana gudanar da wannan taron ne ta hanyar halartar malamai da kuma masu jawabi gami da masu sauare, amma a wanna shekara taron ya gudana ne ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, saboda yanayi na kiwon lafiya da kuma kiyaye yaduwar cutar korona.

Haka nan kuma an buga dukkanin makalolin da aka gabatar a wanann taro, inda aka saka su a cikin babban shafin cibiyar da ke daukar nauyin shirya wadannan taruka.

3952927

 

captcha