IQNA

Al-Sisi Ya Bayar Da Umarnin Cire Ayoyin Kur’ani Da Hadisai A Cikin Wasu Darussa A Makarantu

22:08 - February 18, 2021
Lambar Labari: 3485665
Shugaban kasar Masar Abdulfattah Al-sisi ya bayar da umarni cire ayoyin kur’ani da hadisan ma’aiki (SAW) a cikin wasu darussa guda biyu a makarantu.

Shafin yada larabai na Arabic 21 ya bayar da rahoton cewa, Redha Hijazi mataimakin ministan ilimi a kasar Masar ya sanar da cewa, shugaban kasar ta Masar Abdulfattah Al-sisi, ya bayar umarni cire ayoyin kur’ani da hadisan ma’aiki (SAW) a cikin darussan harshen larabci da kuma tarihi daga cikin manhajar karatu a kasar.

Shi ma a nasa bangaren Faridi Albayadhi, mamba a majalisar koli ta tsaron kasa a Masar ya bayyana cewa, shugaba Abdulfattah Al-sisi ya bayar da wannan umarni ne domin kada masu tsatsauran ra’ayi su yi amfani da hakan, wajen yada akidar ta’addanci da sunan addini.

Sai dai masu rajin kare hakkokin dan adam a kasar ta Masar suna da imanin cewa, tun kafin wannan lokacin Al sisi yana da shirin ganin ya cire ayoyin kur’ani daga wasu darussa a cikin manhajar karatu ta kasar.

Baya ga haka kuma yana son ya rage karfin da cibiyar Azhar take da shi, domin rage tasirinta da karfin fada a ji a cikin kasar kan lamurra da suka shafi addini, kamar yadda kuma yake son ya rusa wasu masallatai wadanda suke da alaka da kungiyoyin da yake kira na ‘yan ta’adda, daga ciki hard a na kungiyar ‘yan uwa musulmi.

3954756

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :