IQNA

18:56 - February 24, 2021
Lambar Labari: 3485686
Tehran (IQNA) an samar da wata sabuwar manhajar kur'ani ta wayar salula a cikin harsuna 15 domin amfanin musulmi a watan Ramadan.

Shafin yada labarai na Palestine ya bayar da rahoton cewa, an samar da wata sabuwar manhajar kur'ani ta wayar salula a cikin harsuna 15 a Falastinu, domin amfanin musulmi a watan Ramadan mai alfarma.

Wanann manhaja dai ta kunshi dukkanin surorin kur'ani mai tsarki, kamar yadda kuma za a iya yin amfani da ita wajen karatu kai tsaye daga mataki, ko kuma sauraren karatun tare da zaben dukkanin makarancin da ake bukata daga cikin jerin makaranta kur'ani da ke cikin manhajar.

Baya ga haka kuma ana iya duba tafsirin kowace aya ake bukata a cikin manhajar, kamar yadda kuma babu bukatar sai an yi amfani da intanet wajen shiga cikin manhajar, matukar dai an sauke ta a kan wayar salula.

Sannan kuam manhajar tana da wani tsari wanda makafi za su iya sauraren tilawar kur'ani a cikinsa, kamar yadda kuma an sanya dukkanin bangarori an manhajar su zama masu saukin budewa ga kowa.

3955742

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: