IQNA

23:58 - March 15, 2021
Lambar Labari: 3485746
Tehran (IQNA) wasu masu kin jinin musulunci sun kona wata makarantar musulmi kasar Sweden

shafin yada labarai na Mujtama'a ya bayar da rahoton cewa, a jiya wasu masu kin jinin musulunci sun kona wata makarantar musulmi kasar Sweden.

Daraktan makarantar ya bayyana cewa, kamarorin da aka saka a makarantar sun dauki hotuna na dukkanin abin da ya faru, kuma yanzu haka an mika wa 'yan sandan kasar ta Sweden dukkanin abubuwan da kamarorin suka dauaka domin yin bincike.

A ciki dai an ga wasu mutane biyu da suka rufe fusakunsu sun iso wurin, da jijjifin safya, daga nan kuma suka fara farfasa gilassai na tagogi da kofofi, daga bab kuma suka fara jefa wasu abubuwa da suke da wuta, wanda hakan ya yi sanadiyyar konewar wasu ajujuwan karatu.

Amma dai a cewar bayanin daraktan makarantar, babu wanda ya rasa ransa ko jikkata, kasantuwar malamai da dalibai ba su fara isowa ba lokacin da lamarin ya faru.

 

3959705

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: makara ، musulmi ، kin jinin ، jiya ، rahoto
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: