
Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Muhammad Abdulsalam daga cikin jagororin kungiyar Ansarullah a Yemen ya bayyana cewa, ba za su amince da duk wani sharadi daga gwamnatin Saudiyya wanda zai cutar da al’ummar Yemen ba.
Ya bayyana cewa batun kawo karshen killacewar da Saudiyya take yi wa kasar Yemen ba batu da za a amince da wani sharadi na siyasa ko na soji a kansa ba, dole ne a kawo karshen killace kasar Yemen ba tare da wani sharadi ba.
Haka nan kuma batun bude manyan filayen jirgin sama na San’a da kuma tashar ruwa ta Hudaidah, da bari a shigo da abinci da kayan bukatar rayuwar al’umma, lamari ne da ya zama wajibi a aiwatar da shi ba bias wani sharadi na siyasa ba.
Shi ma a nasa bangaren shugaban majalisar koli ta juyin juyi a kasar Yemen Muhammad Ali Alhuthy ya bayyana cewa, maganganun mahukuntan masarautar Al Saud ke yi kan batun dakatar da kaddamar da hari kan al’ummar Yemen farfaganda ce kawai, domin kuwa babu wani bayani da gwamnatin San’a ta samu kan hakan a hukumance, sai dai a kafofin yada labaran Saudiyya da kawayenta ake jin hakan.