IQNA

Wani Kirista Yana Gayara Lasifikokin Masallatai Kyauta Saboda Karatowar Watan Ramadan A Masar

23:51 - March 28, 2021
Lambar Labari: 3485769
Tehran (IQNA) wani kirista daga lardin Alfuyum na kasar Masar yana gyara lasifikokin masallatai kyauta saboda karatowar watan Ramadan.

Shafin jaridar Al-dastur ta kasar Masar ya bayar da rahoton cewa, Mahrus Najib wani kirista ne daga lardin Alfuyum na kasar Masar, wanda yake gyara lasifikokin masallatai kyauta saboda karatowar watan Ramadan mai alfarma.

Abin da wannan kirista yake yi babban misali ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinin kirista da kuma musulmi a yankin na Alfuyum da ke kasar Masar.

Mahrus Najib dan shekaru 65 da haihiwa ya bayyana cewa shekaru 27 kenanan yana aikin sayar da lasifikoki da kuma gyaransu awannan yanki, inda yace yana da kyakkyawar alaka da manyan malamai na musulmi na yankin.

Ya ce da dama daga cikin limaman masallatai suna kawo gyaran lasifikokin masallatai a wurinsa, a kan sakamakon karatowar watan azumin Ramadan, ya mayar da gyaran lasifikokin masallatai kyauta.

Ya kara da cewa yana yin farin ciki matuka a duk lokacin da aka shiga watan Ramadan, saboda lokaci ne na rahama da albarka, domin kuwa wata ne da musulmi suke gudanar da ibadar azumi da karatun kur’ani da salloli.

3961494

 

 

 

 

captcha