IQNA

Ranar 15 Ga Watan Sha'aban Ranar Haihuwar Imamul Mahdi (AS)

14:23 - March 29, 2021
Lambar Labari: 3485770
Tehran (IQNA) Imam Mahdi (AS) shi ne limami na 12 daga cikin limaman Ahlul bait (AS) wanda kuma yau 15 ga watan sha'aban ya yi daidai da ranar haihuwarsa.

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai

Za mu fara ne da takaitaccen tarihin Imam Muhammad dan Hasan Al-Mahdi Al-Muntazar {a.s}. Jagoran shiriya na goma sha biyu daga cikin jerin jagororin shiriya da manzon tsira Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} ya yi bushara da samuwarsu a bayansa, kuma ya bayyana kasantuwarsu da daukakar addinin musulunci, sannan ya rubanyasu da alkur'ani mai tsarki saboda tsarkakansu, zuriya tsarkaka da Allah madaukakin sarki ya sanya kaunarsu ta zame sakamakon dawainiyar da manzonsa kuma fiyayyen halitta a wajensa yayi wajen isar da sakon addinin musulunci, zuriya tsarkaka da Allah ya tsarkakesu daga duk wata dauda tsarkakewa, wajen saukan sakonni daga All..., tushen ilimi kuma mabubbugar hikima, shi ne Imam Muhammad dan Hasan Al-Mahdi Al-Muntazar {a.s}.

Imam Muhammad Al-Mahdi Al-Muntazar {a.s} ya fito ne daga tsatson gidan Annabci, zuriya madaukakiya da ta samar da madaukaka a tsakanin al'umma. Hakika zuriyar gidan manzon Allah da Imam Muhammad Al-Mahdi Al-Muntazar {a.s} ya fito daga cikinta, zuriya ce da Allah madaukakin sarki ya daura mata alhakin banbance tsakanin gaskiya da karya da daura al'ummah kan hanyar shiriya tare da fayyace mata hukunce-hukuncen shari'a a bayan manzonta Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w}, don haka ta kasance mafaka ga masu neman shiriya.An haifi jagoran shiriya na goma sha biyu Imam Muhammad dan Hasan Al-Mahdi {a.s} a tsakiyan watan sha'aban shekara ta dari biyu da hamsin da biyar ne {b.h} a garin Samarrah da ke kasar Iraki wanda shi kadai ne a wajen mahaifinsa kamar yadda malaman tarihi suka ruwaito.

Mahaifin Imam Muhammad Al-Mahdi {a.s} shi ne jagoran shiriya na goma sha daya daga cikin jagorori goma sha biyu da manzon Allah ya yi bushara da samuwarsu a bayansa. Imam Hasan Al-Askari {a.s} jagora ne da ya gudanar da dukkanin rayuwarsa wajen wayar da kan mutane tare da ilimatar da su, domin daya ne daga cikin zuriyar gidan Annabci da ta kasance tana rayar da ilimi da kawar da jahilci a tsakanin al'ummah.Mahaifiyar Imam Muhammad Al-Mahdi {a.s} mace ce da ta kasance madaukakiya da girman matsayi a zamaninta sakamakon kyawawan dabi'unta da halayenta na kirki, wadda ake kiranta da Narjis kuma ana kiranta da Mulaikatu ko Raihanatu wanda ya ce ga Yushu'an dan Qaisar sarkin Rum wanda ta hada dangantaka da kebantattun sahabban Annabi Isah {a.s} wato "Hawariyun" daga tsatson Sham'un wasiyin Annabi Isa Almasihu {a.s}kamar yadda ya zo cikin littafin Raudhatul-Wa'izin. Ana kinaya wa Imam Muhammad Al-Mahdi Al-Muntazar {a.s} da Abu-Qasim irin kinayar kakansa manzon Allah {s.a.w} kamar yadda sunansu iri daya.

Kuma yana da lakabi kamar haka:- Al-Mahdi, Alka'im, Almuntazar, Sahibul-Amri da Alhujjah. Haihuwar Imam Muhammad Al-Mahdi {a.s}.Sheikhus-Suduk a cikin littafinsa na Kama'luddeen wa-Tama'mul-Ni'imah ya nakalto fadin Hakimaha€yar Imam Muhammad Jawad {a.s} da ta ke bayyana cewa: Imam Hasan Al-Askari {a.s} ya aike mata da sakon cewa: Ya goggo muna gayyatarki sha ruwa a gidanmu a wannan dare, inda wannan daren ya yi daidai da tsakiyar watan sha'aban, sannan Imam Hasan Al-Askari {a.s} ya ke ba ta labarin cewa: Hakika a wannan dare ne za a haifi hujjan Allah a bayan kasa, wannan da Allah Madaukakin Sarki da Buwaya zai rayar da kasa da shi bayan mutuwarta.Sai Hakimah ta ke tambayar Imam Hasan Al-Askari {A.S} wace ce daga cikin matarka zata haifeshi? Sai Imam Askari ya amsa mata da cewa: Narjis. Amma da Hakimah ta shiga wajen Narjis ba ta ga alamar tana dauke da ciki ba, sai ta dawo wajen Imam Hasan Al-Askari ta ce masa: Allah ya sanyani na zame fansanka: Babu alamar ciki tare da Narjis, sai Imam Askari yayi murmushi yake bayyana mata cewa: Kamar yadda na furta miki, ita ce zata haifeshi a wannan dare.Hakimah ta ci gaba da cewa: Bayan ta idar da sallah ta sha ruwa, ta dan kishingida domin ta hutu, sannan cikin dare ta mike ta gudanar da sallar dare har kusan fitowar alfijir amma ba ta ga wata alamar nakuda tare da Narjis ba, sai zuciyarta ta fara kokwanto, amma sai ta ji muryar Imam Hasan Al-Askari {A.S} da yake wani daki da ke makobtaka da wadda suke ciki yana cewa: Ya goggo ka da kiyi gaggawa, tabbas lamarin ya karato. Jin wannan furuci daga Imam Hasan Al-Askari {A.S} sai kunya ta kama Hakimah.Bayan dan wani lokaci sai Hakimah ta ga Narjis cikin wani hali, don haka ta ke tambayarta ko ta fara jin alamar nakuda ce da ta bayyana mata, sai Narjis ta amsa da cewa tabbas goggo ina jin alamar nakuda mai tsanani tare da ni, saboda haka Hakimah ta gudanar mata da shirye-shiryen mai haihuwa, har lokacin da haihuwar ta karato, Narjis ta rike hannuwar Hakimah tana nishi mai tsanani na haihuwa, don haka Imam Hasan Al-Askari {A.S} ke cewa Hakimah ta karanta Suratul-Qadir. Hakimah ta ce tana fara karanta Suratul-Qadir kamar yadda Imam Askari {A.S} ya umurceta, sai ta ji jaririn da ke cikin Narjis yana bitar karatun da ta ke yi, sakamakon haka Hakimah ta razana, amma sai ta ji muryar Imam Hasan Al-Askari {A.S} yana cewa: Ka da mamaki ya kamaki daga al'amarin Allah Madaukaki, domin hakika Allah yana bude bakinmu da hikima a lokacin da muke kananan yara, kuma ya sanyamu hujjojinsa a bayan kasa bayan girmanmu.Hakimah ta kara da cewa: Bayan dan wani lokaci sai ta ankara ta ga alamar kyalle dake tsakaninta da Narjis yana motsi, tana dagawa sai ta ga haske ya dauke mata ido, jariri a kasa yayi sujjada a kan gabobinsa cikin tsarki kamar ba a lokacin aka haifeshi ba, ganin haka Hakimah ta daukeshi ta rungumeshi domin murna da farin ciki.

Sai Hakimah ta ji Imam Hasan Al-Askari {a.s} yana cewa: Miko mini dana ya goggo, don haka ta zo da shi wajen mahaifinsa, inda ya karbeshi ya sanya harshensa cikin na dansa, sannan yake ce masa yi magana: Ya dana, sai jaririn yayi furuci da kalmar shahada da salati ga Manzon Allah da jagororin shiriya na iyalan gidansa tsarkaka tare da ambaton sunayensu daya bayan daya har ya zo kan sunan mahaifinsa, sannan ya yi isti'aza da basmala ya karanta fadin Allah Madaukaki da ke cewa: {Kuma muna nufin mu yi falala ne ga wadanda aka raunanar a bayan kasa, kuma mu sanya su shugabanni kuma mu sanya su magada.

Kuma mu tabbatar da su a bayan kasa, kuma mu nuna wa Fir'auna da Hamana da rundunoninsu abin da suka kasance suna tsoron faruwarsa}.Sannan Imam Hasan Al-Askari {a.s} yake cewa Hakimah: Ya goggo karbeshi ki mai da shi ga mahaifiyarsa domin ta yi farin ciki, hakika alkawarin Allah gaskiya ne, sai dai mafi yawan mutane ba su sani ba.

Hakimah ta dauki jaririn ta mai da shi ga mahaifiyarsa wanda a lokacin alfijir ya riga ya fito, bayan sallah sai Hakimah ta yi bankwana da Imam Hasan Al-Askari {a.s} ta koma gidanta.

Shekarun Imam Muhammad Al-Mahdi Al-Muntazar a lokacin da ya karbi ragamar jagoranci al'umma a bayan mahaifinsa Imam Hasan Al-Askari {a.s}.

Imam Muhammad Al-Mahdi Al-Muntazar {A.S} ya karbi ragamar jagoranci ne a lokacin yana da shekaru biyar a duniya, don haka shi ne wanda ya fi karancin shekaru a lokacin da ya karbi ragamar jagoranci a tsakanin jagororin shiriya na iyalan gidan Manzo, kamar yadda hadisai da dama suka yi nuni da haka.

Misalin hadisin da aka ruwaito daga Imam Muhammad Baqir {A.S} da ke cewa: Ma'abucin wannan lamari shi ne wanda ya fi mu karancin shekaru a lokacin da ragamar jagoranci zai koma gare shi.

Hakika hakan ba abin da zai bada mamaki ba ne musamman ga wanda ke da masaniya kan tarihin Annabawa da Manzonnin Allah da Jagororin shiriya na iyalan gidan manzo {A.S}, domin a cikinsu an samu wadanda suka karbi ragamar shiryar da al'ummah a kasa da shekarun Imam Muhammad Al-Mahdi {A.S}, kamar yadda nassin alkur'ani mai girma ya tabbatar da haka a kan Annabi Isah da Yahaya {A.S}, kuma a bangaren iyalan gidan Manzon Allah {S.A.W} Imam Muhammad Jawad da dansa Imam Ali Al-Hadi {A.S} dukkaninsu sun karbi ragamar jagorancin al'ummah ne suna da karancin shekaru.

Alkur'ani mai girma ya bamu labarin cewa: Allah Madaukaki ya aiko Annabi Yahaya da sakon annabci ne tun yana karamin yaro da cewa:- {Ya kai Yahaya, ka riki littafi da karfi, kuma muka bashi hukunci yana karamin yaro}.Dangane da Annabi Isa dan Maryam kuwa, alkur'ani mai girma yana cewa:- {Sai ta yi nuni zuwa gare shi, suka ce, yaya za mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfidar tsummar haihuwa yana jariri.

Ya ce, hakika ni bayan Allah ne, Allah ya ba ni littafi kuma ya sanya ni Annabi. Kuma ya sanya ni mai albarka a duk inda na kasance, kuma ya umurceni da yin sallah da bada zakkah matukar ina raye}.

Matakin da Imam Muhammad Al-Mahdi Al-Muntazar {a.s} ya dauka na bayyana samuwarsa ga mabiyansa bayan shahadar mahaifinsa Imam Hasan Al-Askari {a.s}.

Farkon aikin da Imam Muhammad Al-Mahdi {a.s} ya fara aiwatarwa bayan karbar ragamar jagorancin shiryar da al'ummah a bayan shahadar mahaifinsa shi ne: Gudanar da sallar jana'iza ga mahaifinsa Imam Hasan Al-Askari {a.s} a cikin gida, kafin fito da gawar mai tsarki waje domin gudanar mata da sallar jana'iza kamar yadda mahukunta daular Abasiyawa suka shirya a hukumance.

Hakika wannan mataki da Imam Muhammad Al-Mahdi {a.s} ya dauka na gudanar da sallar jana'iza ga mahaifinsa Imam Hasan Al-Askari {a.s} mataki ne da ke kara tabbatar da kasancewarsa jagoran shiriya a bayan mahaifinsa, duk kuwa da hatsarin da zai fuskanta idan labari ya watsu cewa shi ya gudanar da sallar jana'iza ga mahaifinsa bayan shahadarsa, sakamakon tsaurara matakan da mahukuntan daular Abasiyawa za su dauka wajen farautarsa domin kawo karshensa a kokarin da suke yi na ganin sun hana samuwar tsayayye daga zuriyar gidan Manzon Allah da zai zo ya kawar da duk wani nau'in zalunci da babakere domin shimfida tsarin adalci da daidaito a tsakanin al'ummah.

Dalilan da suke tabbatar da bayyanar Imam Muhammad Al-Mahdi {a.s} a littattafan malaman ahlus-sunna.

Kasancewar imani da Imam Mahdi {a.s} yana daga cikin tushen akidar mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah {s.a.w} saboda haka babu wani dan shi'a da yake kokwanto kan samuwarsa, don haka zamu takaita ne da ambaton kadan daga cikin hadisan da malaman ahlus-sunnah waj-jama'a suka nakalto a cikin littattafansu kan batunsa {a.s} kamar haka:-Imam Abu-Daud Sulaiman Dan Ash'as Azdiyi a cikin littafin hadisinsa na Sunan Abi-Daud ya nakalto fadin Manzon Allah {s.a.w} da ke cewa: Da babu abi da ya yi saura a zamani sai kwana daya tak da Allah ya ta da wani mutum daga iyalan gidana da zai cika kasa da adalci kamar yadda zalunci ya cikata.

Abu-Daud ya kuma nakalto fadin Uwar muminai Ummu Salmah da ta ke cewa ta ji Manzon Allah {s.a.w} yana cewa: Al-Mahdi daga zuriyata yake daga tsatson Fatimah.Abu-Isah Muhammad dan Isah dan Surata dan Musa Attirmiziyu a cikin littafin hadisinsa na Sunanul-Tirmizi ya nakalto fadin Manzon Allah {s.a.w} da ke cewa: Duniya ba za ta kawo karshe ba har sai wani mutum daga iyalan gidana sunansa irin nawa ya shugabanci larabawa.

Shi ma Hafiz Abu-Abdullahi Muhammad dan Yazidu Alkazwini a cikin littafin hadisinsa na Sunan Ibnu Majah ya nakalto fadin Ali dan Abi-Talib da ke cewa: Manzon Allah {s.a.w} ya ce: Mahdi daga garemu yake Ahlul-Baiti.

Ahmad dan Muhammad dan Hanbal a cikin littafin hadisinsa na Musnad Ahmad ya nakalto fadin Manzon Allah {s.a.w} da ke cewa: kasa zata cika da zalunci da babakere sannan wani mutum daga zuriyata ya bayyana da zai yi shugabanci na shekaru bakwai ko tara, zai cika kasa da adalci da daidaito.

Hakim Annisaburiyyu a cikin littafin hadisinsa na Mustadrak alal-Sahihain ya nakalto fadin Manzon Allah {s.a.w} da ke cewa: Al'ummata zata fuskanci bala'i daga mahukunta a karshen zamani da ba a taba jin bala'i makamancinsa ba, har kasa ta yi musu kunci kuma har kasar ta cika da zalunci da babakere, babu wani waje da mumini zai fake domin samun saukin zalunci, sai Allah madaukaki da buwaya ya ta da wani mutum daga zuriyata da zai cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda zalunci da babakere ya cikata.

Dalilai gami hikimomin da suke kunshe cikin fakuwar Imam Muhammad Al-Mahdi {a.s}.

Abu ne da yake tabbas babu kokwanto cikinsa cewa: Allah Madaukakin Sarki da Buwaya mai hikima ne gwani da baya aikata wani abu da babu hikima da masalaha ciki, inda masalahar ta ke komawa zuwa ga halittu, ba ga zatin Allah mahalicci ba, domin Allah ya wadata ga dukkan wata bukata.

Don haka dukkanin ayyukan Allah Madaukaki suna gudana ne daidai da hikima da masalaha, ko da dan Adam bai kai ga gano tarin hikima da masalahar da ke cikin ayyukan na Allah Madaukaki ba.

A fili yake cewa: Akwai tarin abubuwa da dama da suke kewaye da dan Adam da har ya zuwa yanzu bai kai ga gano hikima da masalahar samuwansu ba, kuma a haka abubuwan za su ci gaba da gudana cikin jahilcinsa a tsawon zamani.

Yayin da a gefe guda kuma, wasu abubuwan da a baya suka shige duhu ga dan Adam, a halin yanzu ya kai ga gano hikima da masalahar samuwarsu, musamman saboda bunkasar ilimi a tsakanin jinsin bil-Adama.

Amma duk da bunkasar ilimi da ci gaban da dan Adam ya samu a tsarin rayuwarsa, abubuwan da ya sani kuma ya kai ga gano sirrin hikimar samuwarsu, idan aka kwatanta da abubuwan da ya jahilta, sai a hukuntashi da cewa har yanzu bai kai ga sanin wani abu daga cikin sirrin hikimar samuwar abubuwa ba. Idan muka kai ga fahimtar haka, to hakika a fakuwar Imam Muhammad Al-Mahdi Al-Muntazar {A.S} da rashin kasantuwarsa a tsakanin mutane akwai tarin hikima da masalaha da suka wajabta fakuwar ta sa daga idon mutane, kuma ko da dan Adam bai kai ga sanin hikima da fahimtar sirrin da ke cikin fakuwar ta sa ba.

Don haka zamu bijiro da wasu daga cikin dalilai da kuma hikimomin da suka sanya Imam Muhammad Al-Mahdi {A.S} ya shiga fakuwa kamar yadda hujjoji na hankali da shari'a suka tabbatar kamar haka:-Hikima ta farko:- Hakika rayuwar Imam Muhammad Al-Mahdi {A.S} tana cikin hatsari mai girma, inda ta kai ga fuskantar barazanar mutuwa ta hakika daga mahukuntan daular Abasiyawa, don haka babu makawa ga Imam Mahdi ya dauki duk wani matakin kare kansa daga salwanta, sakamakon haka ya dauki matakin buya ta hanyar shiga fakuwa daga idon mutane.

Hikima ta biyu:- Kubuta daga mubaya'ar duk wani azzalumi. Hakika fakuwar da Imam Muhammad Al-Mahdi {A.S} ya shiga ya yi sanadiyyar kubutarsa daga mubaya'ar duk wani azzalumin shugaba. kamar yadda fakuwar ta sa ta wadatar da shi daga gudanar da takiya wato boye abin da ya yi imani da shi, ta hanyar bayyana abin da yake sabanin haka, saboda tsoron makircin mahukunta kamar yadda ta wakana da magabatansa jagororin shiriya na iyalan gidan Manzon Allah da suka yi mubaya'a wa azzaluman shugabannin zamaninsu saboda halin tsaka mai wuya da suka shiga a wancan lokacin.Hikima ta uku:- Jarabawa da gwaji.

Hakika yana daga cikin dalilai da hikimar fakuwar Imam Muhammad Al-Mahdi {A.S} daga idon mutane, halin jarabawa da gwajin da bayin Allah za su shiga a lokacin, kamar yadda hadisai suka yi nuni da haka, misalin hadisin da aka ruwaito daga Imam Ja'afar Sadiq {A.S} da ke cewa: Amma wallahi, tabbas jagoranku zai shiga fakuwa na tsawon shekaru domin jarabawa, har a ce ya mutu ko ya halaka, mutane na tambaya ina ya shiga ne, lalle idon muminai zai zubar da hawaye saboda shi, hakika guguwar fitina za ta yi gaba da mutane da dama kamar yadda igiyar ruwa ke yin awungaba da jirage, babu wanda zai tsira sai wanda Allah ya karbi alkawarinsa, ya rubuta imani a cikin zuciyarsa, kuma ya karfafa shi da ruhi daga gare shi.

Hikima ta hudu:- Yana daga cikin dalilai gami da hikima da suka sanya Imam Muhammad Al-Mahdi {A.S} shiga halin fakuwa, nisantar azzalumai tare da kaurace musu.Hikima ta biyar:- Hakika fakuwar Imam Muhammad Al-Mahdi {A.S} daga idon mutane yana daga cikin sirrin Allah madaukaki, kamar yadda ya zo cikin hadisin manzon Allah {S.A.W} cewa: Iyaka misalin fakuwarsa wato Imam Mahdi kamar misalin ranar kiyama ce, da tayi nauyi wa sammai da kassai da ba zata zo muku ba sai kwatsam babu shiri.

 

captcha