IQNA

A Karon Farko Joe Biden Ya Mika Sunan Wani Alkali Musulmi Domin Nada Shi Alkalin Kotun Tarayya

14:48 - April 01, 2021
Lambar Labari: 3485775
Tehran (IQNA) shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da sunan wani alkali musulmi domin nada shi a matsayin alkalin kotun tarayyar a jihar New Jersey.

Tashar Geo TV ta bayar da rahoton cewa, a karon farko shugaban kasar Amurka Joe Biden ya gabatar da sunan wani alkali musulmi domin nada shi a matsayin alkalin kotun tarayyar a jihar New Jersey da ke kasar ta Amurka.

Zahed Quraishi musulmi ne dan asalin kasar Pakistan, kuma alkali a jihar New Jersey ta kasar Amurka, wanda kuma idan aka amince da bukatar Joe Biden, zai zama alkalin kotun tarayyar Amurka musulmi na farko a tarihi.

‘Yan majalisar wakilai da kuma na dattijan Amurka daga jihar New Jersey sun yi godiya kan wannan mataki na Joe Biden, kamar yadda kwamitin habbaka alaka tsakanin Amurka  da Pakistan ya jinjina wa shugaba Biden kan hakan.

Kafin wannan lokacin dai Joe Biden ya nada wasu musulmi da kuma bakaken fata da yawa a kan mukamai a cikin gwamnatin Amurka tun bayan da aka rantsar da shi a kan kujerar shugabancin kasar.

A shekara ta 2019 ne aka nada Quraishi a matsayin alkali a jihar New Jersey wanda kafin lokacin farfesa na jami’a a bangaren koyar da ilimin shari’a.

 

3961867

 

 

 

captcha