IQNA

Amnesty International Ta Yi Gargadi Kan Cin Zalun Da Isra’ila Take Yi A Kan Falastinawa

20:06 - April 07, 2021
Lambar Labari: 3485792
Tehran (IQNA) kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta yi gargadi kan cin zalun da Isra’ila take yi akan Falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran SAFA ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani rahoto da ta fitar, kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta yi gargadi kan cin zalun da Isra’ila take yi akan Falastinawa a cikin yankunansu da ta mamaye.

Wannan rahoto dai an shirya shi ne kan ayyukan zaluncin Isra’ila a kan Falastinawa a cikin shekara ta 2020 da ta gabata, wanda ya tabbatar da cewa, a cikin wannan shekara Isra’ia ta rusa gidajen Falastinawa guda 848.

Ofishin majalisar dinkin duniya da ke Falastinu ya bayar da bayanin cewa, wasu gidaje 200 da Isra’ila ta kori Falastinawa da suke da su, hakan ya yi sanadiyya jefa kananan yara kimanin 800 cikin mawuyacin halai, saboda mahaifansu ba su da inda za su tsugunna, saboda Isra’ila ta kore daga gidajensu.

Kungiyar ta Amnesty ta ce dole ne kasashen duniya su takawa yahudawan Isra’ila burki dangane da zaluncin da suke yi kan al’ummar Falastinu, tare da bawa Falastinawan damar kafa kasarsu mai cin gashin kanta.

3963071

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha