IQNA

Wasu Da Ba A San Ko Su Wane Ne Sun Banka Wa Wani Masallacin Musulmi Wuta A Faransa

21:56 - April 10, 2021
Lambar Labari: 3485795
Tehran (IQNA) wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun banka wa wani masallacin musulmi wuta a kasar Faransa.

Shafin yada labarai na rasad ya bayar da rahoton cewa, jami’an ‘yan sanda na birnin Nante da ke kasar Faransa sun sanar da cewa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun banka wa wani masallacin musulmi wuta a birnin.

Bayanin ya ce, mutanen sun yi amfani da wasu rubobi ne da suka cika da takardu da kuma makamashi, inda suka sanya musu wuta, sannan suka jefa a kan masallacin.

Babban kungiyar musulmi ta kasar Faransa CFCM ta fitar da bayani, wanda a ciki ta yi Allawadai da kakakusar murya kan wannan mummunan aiki.

A nasu bangaren mahukunta  akasar Faransa sun sanar da cewa, sun fara gudanar da bincike kan lamarin, domin gano wadanda suke ad hannu a wannan aiki domin su fuskanci hukunci.

Ministan harkokin cikin gida na kasar ya bayyana bakin cikinsa kana bin da ya faru, tare da bayyana goyon bayansu ga musulmi dangane da abin da yake faruwa a kansu a kasar ta Faransa.

 

3963529

 

 

 

captcha