IQNA

An Fara Gasar Karatun Kur'ani Ta Masu Fama Larura A birnin Dubai

23:55 - April 18, 2021
Lambar Labari: 3485823
Tehran (IQNA) an fara gasar karatun kur'ani mai tsarki ta masu fama da larura a birnin Dubai na UAE.

Shafin yada labarai na Albayan ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne fara gasar karatun kur'ani mai tsarki ta masu nasaka a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa.

Mutane 330 ne suke halartar wannan gasa, wadanda dukkaninsu ko dai suna fama da larurar gani, ko kuma larurar ji koma tawaya a wasu bangarorin jikinsu, inda suke karawa da juna a wannan gasa.

Gasar ta hada da hardar kur'ani juzu'i 20, ko 15, ko 10, ko 7 ko 5 ko kuma 3 ko 2 ko kuma daya, ko wasu daga cikin gajerun surorin kur'ani mai tsarki.

Babbar manufar shirya wannan gasar dai ita ce karfafa gwiwar masu fama da larura kan lamarin kur'ani, ta yadda za su ji cewa za su iya yin komai da ya shafi addini kamar sauran masu lafiya daidai iyawarsu.

 

3965362

 

 

 

captcha