IQNA

Majalisar Wakilan Amurka Ta Amince Da Kudirin Hana Shugaban Kasa Kafa Dokar Hana Shiga Kasar Saboda Addini

17:38 - April 22, 2021
Lambar Labari: 3485835
Tehran (IQNA) majalisar wakilan Amurka ta amince da wani kudiri da ke hana shugaban kasa kafa dokar hana shiga kasar saboda addini.

tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan kaddamar da wani kamfe mai taken (No Ban Act) da ke neman majalisa ta dauki matakin hana duk wani shugaba a Amurka kafa dokar hana shigar mutane a kasar saboda addininsu.

Wannan daftarin kudiri ya samu amincewar ‘yan majalisa 218, dukkaninsu ‘yan jam’iyyar Democrat, yayin da kuma wasu ‘yan majalisa 208 dukkaninsu ‘yan jam’iyyar Republican suka ki amincewa da daftarin kudirin.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da kungiyoyin farar hula na kasar sun yi na’am da wannan kudiri, tare da bayyana shi a matsayin nasara ga masu yunkurin son ganin an yi adalci.

Madihha AHussain daya ce daga cikin lauyoyi masu gwagwarmayar kare hakkokin bil adama a kasar Amurka, ta bayyana wannan matakin da cewa yana da muhimmanci, domin kuwa zai kawo karshen nuan wariya da ake yi wa musulmi a hukumance, inda shugaban kasar Amurka da ya sha kayi a zabe Donald Trump ya mayar da hakan ya zama doka a hukumance.

A cikin shekara ta 2017 ne dai tsohon shugaban na Amurka ya kafa wannan doka ta hana wasu mutane daga wasu kasashe shiga Amurka saboda addini, yayin da kuma ya hana wasu saboda takun sakar siyasa da ke tsakanin Amurka da gwamnatocin wadannan kasashe.

3966433

 

Abubuwan Da Ya Shafa: daftarin kudiri
captcha