IQNA

Ministan Yakin Isra’ila Ya Yarda Cewa Isra’ila Ta Kasa Tare Makami Mai Linzami Daga Syria

23:35 - April 23, 2021
Lambar Labari: 3485839
Tehran (IQNA) ministan yakin Isra’ila ya amince da cewa makaman kariyar Isra’ila sun kasa tare makami mai linzami da harbo daga Syria.

A cikin bayanin da ya yi, ministan yakin Isra’ila Bani Gatz ya bayyana cewa, hakika makaman kariya na Isra’ila sun gaza tare makamin da harbor daga Syria a kusa da bababr tashar nukiliya ta Isra’ila da ke Dimona.

Ya ce sun yi kokarin ganin ganin sun tare wannan makami mai linzami, da aka harba a jiya Alhamis, amma dai makamansu sun gaza tare shi, inda ya ce lallai a halin yanzu babu tabbaci kan makaman kariyar Isra’ila.

Ministan yakin na Isra’ila ya ci gaba da cewa, a halin yanzu sun dukufa wajen gudanar da bincike kan wannan lamari, domin gano inda aka samu matsala a tsarin makaman kariya na Isra’ila.

Shi ma a nasa bangaren tsohon ministan yakin Isra’ila Abigdor Libarman ya bayyana cewa, abin ya faru ya nuna gazawar Isra’ila ta fuskar tsaro, kuma ya dora alhakin hakan a firayi ministan gwamnatin yahudawan Benjamin Netanyahu, domin kuwa hakan ya faru ne kwana daya bayan tarwatsewar wata wata cibiyar kera makamai masu linzami ta Isra’ila.

Tuni dai Isra’ila ta dora alhakin abin da ya faru a kan Iran, yayin da ita kuma Iran ta bayyana cewa, abin da ya faru ya kara tabbatar wa duniya cewa karfin  kuri na baki kawai.

 

3966517

 

 

 

captcha