IQNA

Malam Azahar Sun Mayar Da Martani Kan Laifukan Yakin Israila A Falastinu

22:47 - May 17, 2021
Lambar Labari: 3485924
Tehran (IQNA) wasu daga cikin cikin manyan fitattun cibiyar Azhar sun mayar da martani mai zafi kan laifukan yakin da Isra’ila take tafkawa kan al’ummar Falastinu.

Shafin yada labarai na Bawwabah Veto ya bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin cikin manyan fitattun cibiyar Azhar sun mayar da martani mai zafi kan laifukan yakin da Isra’ila take tafkawa kan al’ummar Falastinu da wurare masu tsarki.

Tsohon babban malami mai bayar da fatawa na kasar Masar sheikh Ali Juma’a ya bayyana cewa, yanzu ba maganar yin Allawadai da mamaye Quds ko hari a Gaza ne kawai ake bukata ba, babban abin da ked a muhimmanci shi ne kawo karshen mamayar yahudawan sahyuniya a kan Falastinu.

Ya ce mamayar Isra’ila a kan kasar Falastinu shi ne ummul haba’isin dukkanin wadannan laifukan yaki da take tafkawa.

3971982

 

captcha