IQNA

Tsoho Mai Kimanin Shekaru 100 Makaranci Kuma Mahardacin Kur'ani Mai Tsarki

23:51 - June 13, 2021
Lambar Labari: 3486009
Tehran (IQNA) Haji Sulaiman Sayyid Sulaiman Dawud tsoho dan kimanin shekaru 100 a kasar Masar, makaranci kuma mahardacin kur'ani mai tsarki.

Jaridar Akhbar Yaum ta bayar da rahoton cewa, Haji Sulaiman Sayyid Sulaiman Dawud tsoho dan kimanin shekaru 100 a kasar Masar, makaranci kuma mahardacin kur'ani mai tsarki, wanda har yanzu duk da tsufa da ya riske shi, amma yana ci gaba da koyar da dalibansa da tarbiyantarsu tarbiya ta kur'ani mai girma.

Sayyid Sulaiman yana daga cikin dadaddun makaranta kur'ani da suka shahara a lardin Manufiyya na kasar Masar, inda tun fiye da shekaru 75 da suka gabata yake koyar da dalibai karatu da hardar kur'ani, kuma har yanzu bai fasa ba, duk da cewa shekarunsa sun kai kimanin 100 a duniya.

Ya yi aiki tare da cibiyar Azahar, kamar yadda kuma ya yi tare da ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar, amma ya yi ritaya daga shekaru masu yawa da suka gabata.

 Kowace rana yana fara bayar da darasin kur'ani ne a masallacinsa da zaran an kammala sallar asubahi, inda daruruwan dalibansa suke taruwa domin daukar karatu.

 

3977042

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tsoho dan shekaru kimanin 100 ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :