IQNA

A Karon Farko Daliba Musulma Ta Zama Shugabar Kungiyar Daliban Jami'a A Amurka

22:12 - June 21, 2021
Lambar Labari: 3486037
Tehran (IQNA) a karon farko wata daliba musulma ta zama shugabar kungiyar daliban jami'ar Yale da ke Amurka tun bayan kafa jami'ar a shekaru 320 da suka gataba.

Shafin yanar gizo na tashar Aljazeera ya bayar da rahoton cewa, a karon farko wata daliba musulma da lullubi a kanta ta zama shugabar kungiyar daliban jami'ar Yale tun bayan kafa wannan jami'ar a shekaru 320 da suka gataba a kasar Amurka.

Dalibar mai suna Bayan Jalal da farko ta kasance shugabar kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya na kungiyar daliban jami'a, ganin irin namijin kokarin da ta yi wajen taimaka ma dalibai musamman a lokacin kullen corona, wannan ya sanya ta samu karbuwa matuka a tsakanin dalibai, wanda daga karshe dukkanin dalibai suka amince a kan ta karbi shugabancin kungiyarsu.

Jalal ta ce, duk da matsaloli da kalubale da musulmi suke fuskanta a cikin wasu lamurra a kasar Amurka, a kowane lokaci tana kokarin ganin cewa ta shiga gaba a cikin lamurra da dama a matsayinta na musulma wadda take yin riko da addini, domin tabbarwa mutane a Amurka cewa musulmi ba a baya suke ba, za su iya taka kowace irin muhimmiyar rawa a dukkanin bangarori na ci gaba.

Ta ce a lokacin kullen corona, ita da wasu daga cikin dalibai musulmi sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen taimaka ma mutane, inda sukan nemi taimamko daga cibiyoyi daban-daban domin taimaka wadanda suke bukatar taimako, da hakan ya hada da na abinci magunguna kudi da dai sauransu, wanda hakan ya yi tasiri matuka, musamman ganin cewa kowa ya san cewa su musulmi ne suke gudanar da wanann aikin.

 

3978840

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :