Shafin jaridar Alkhabar ta kasar Aljeriya ya bayar da rahoton cewa, kungiyoyi da cibiyoyi guda 47 a kasar Jamus sun sanar da cewa ba su amince da cin zarafin musulmi ba kuma dole ne a dauki matakin kawo karshen hakan a kasar Jamus.
Kungiyoyi 47 masu adawa da nuna wariya ko kin wani jinsin mutane saboda addini, sun sanar da cewa, daga yanzu ba za su sake amincewa da duk wani mataki na nuna adwa ko kin jini ga musulmi a kasar ta Jamus ba.
Shugaban kwamitin musulmin kasar Jamus Abdulsamad Al-yazidi ya bayyana cewa, bisa alkalumman da jami'an tsaron kasar suka fitar, an kai wa musulmi hari ko cin zarainsu sau 950 a cikin shekara ta 2020 da ta gabata.
Idan ba a manta ba a ranar 1 ga watan Yulin 2009, Marwa Sharbini wata likita musulma 'yar kasar Masar ta yi shahada, a lokacin da wani mai tsananin kiyayya da musulunci dan kasar Jamus ya yi ta daba mata wuka a gaban kotu, bayan da ta kai kararsa kan cin zarafinta da yake yi saboda saka tufafi irin na muslunci da take yi.