IQNA

Sheikh Ahmad Tijani Jagoran Mabiya Mazhabar Ahlul Bait (AS) A Saliyo Ya Koma Ga Allah

16:11 - June 26, 2021
Lambar Labari: 3486050
Tehran (IQNA) Sheikh Ahmad Tijani Sila babban malamin addinin muslunci jagoran mabiya mazhabar ahlul bait (AS) a kasar Saliyo ya koma ga Allah.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, ajiya ne aka sanar da rasuwar Sheikh Ahmad Tijani Sila babban malamin addinin muslunci jagoran mabiya mazhabar ahlul bait (AS) a kasar Saliyo.

Shehin malamin ya rasu bayan fama da rashin lafiya na wani dan lokaci, inda daga karshe dai rai ya yi halinsa a daren jiya.

Sheikh Ahmad Tijani ya yi karatuna addini na tsawon shekaru masu yawa, daga cikin kasashen da ya je domin karatu akwai kasar Iran, inda ya yi karatu a kasar tun lokacin mulkin sarki Shah, kafin juyin juya halin muslunci a kasar.

Daga bisani bayan samun juyi  a kasar Iran, ya samu kyakkyawar alaka da jami'an kasar, inda akan gayyace taruka daban-daban na kasa da kasa da ake gudanarwa  akasar kan harkoki na addini ci gaban al'ummar musulmi.

Ya yi rubuce-rubuce a bangarori daban-daban na ilimi, kamar yadda kuma ya kasance mai gabatar da jawabai a tarukan daban-daban na addini a ciki da wajen kasar saliyo, yana daga cikin mambobin majalisar malaman addini ta kasar.

Ya gina makarantu da masallatai, kamar yadda kuma kafa gidan rediyo na addini a birnin Freetown fadar mulkin kasar Saliyo, wanda yake yada shirye-shirye na addini da kuma ilmantarwa da fadakarwa.

Musulmin kasar Saliyo da ma wadanda ba musulmi ba, sun shedi da cewa shi mutum ne mai kyawawan halaye da taimakon jama'a da kuma gudanar da ayyikan jin kai, yana taimakon kowa, musulmi da wanda ba musulmi ba.

Ana bangaren gwamnatin kasar Saliyo ta bayyana rasuwar Sheikh Ahad Tijani da cewa babban rashi ne ga dukkanin al'ummar kasar, domin kuwa kasar ta rasa daya daga cikin dattijai da take matukar bukatar irinsu, wadanda suke bayar da gudunmawa domin ci gaba da kuma hada kan al'ummar kasa da bukansa ilimi.

 

 

3980165

 

 

captcha