IQNA

Azhar Za Ta Kafa Wata Makaranta Domin Yada Matsakaicin Ra'ayi Na Addini

22:17 - June 27, 2021
Lambar Labari: 3486054
Tehran (IQNA) babbar cibiyar addinin muslunci ta Azhar a kasar Masar ta sanar da cewa za ta kafa wata makaranta domin yada matsakaicin ra'ayin addini.

Jaridar Ittihad ta kasar Masar ta bayar da rahoton cewa, babban malamin cibiyar addinin muslunci ta Azhar a kasar Masar Sheikh Ahamd Tayyib ya sanar da cewa, cibiyar za ta kafa wata makaranta domin yada matsakaicin ra'ayin addini a tsakanin matasa musulmi.

Bayanin ya ce, makarantar za ta mayar da hankali kan ilmomi na kur'ani da kuma hadisan ma'aiki, tare da koyar da hakikanin ma'anoninsu, ta yadda za a gina malaman kur'ani da hadisi wadanda za su kalubalanci masu yada tsatsauran ra'ayi bisa karkatacciyar fahimta ta addini, wadda ake jingina ta da kur'ani mai tsarki da sunnar manzon allah, wanda kuma bisa hakan ne ake samun akidu an ta'addanci da sunan addini.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, za a kafa makarantar ne bisa dukkanin tsare-tsare na zamani, ta yadda masu karatun za su amfana da sauran bangarori na ilimi.

Da farko dai shirin zai fara ne da daliban ciyar Azhar da ake turawa zuwa birane na kasar Masar ko kasashen ketarea  wasu lokuta na musamman domin yin wa'azi a masallatai da koyar da jama'a ilmomin addini, kafin daga bisa za a fadada shirin wanda zai kunshi dalibai daga wajen cibiyar.

 

3980214

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: makaranta
captcha