
Rahtanni dagakasar Saudiyya na cewa an fara shirin gyaran dakin Ka'abah mai alfarma domin aikin hajjin bana, kamar yadda aka saba gudanar da irin wannan aiki kowace shekara, bayan an kammala dinka sabon kyallen dakin ka'abah, wanda za a yi aikin hajji da shi, wanda ake saka shi da bakin alhariri, sannan a saka farin kyalle a kasansa..
Wannan aiki dai ya hada da masallacin haramin Makka da kuma masallacin manzon Allah (SAW) da ke birnin Madina, inda shi ma ake yi masa gyare-gyare kowace shekara kafin fara aikin hajji.
A shekarar bana dai mutane dubu 60 ne kawai za su gudanar da aikin hajji, kuma dukkaninsu dolle ne su zama suna cikin kasar ta Saudiyya, 'yan kasa ne ko ba 'yan kasa ba.