Tashar Almasirah ta bayar da rahoton cewa, jiragen yakin gwamnatin Saudiyya sun kaddamar da munanan hare-hare a cikin gundumar Sa'adah da ke arewacin kasar Yemen, tare da kashe fararen hula da kuma jikkata wasu.
Rahoton ya ce, baya ga hare-hare ta sama, sojojin Saudiyya sun kaddamar da wasu hare-haren da makaman atilari a kan kauyuka da suke cikin gundumar ta Sa'adah da ke kan iyaka da kasar ta Saudiyya.
Tsawon fiye da makonni biyu kenan a jere Saudiyya tana kaddamar da munanan hare-hare a kan yankuna daban-daban na kasar Yemen, lamarin da ke ci gaba da jawo salwantar rayukan fararen hula, mata da kananan yara.
Wannan na zuwa ne dai a daidai lokacin da Amurka ke da'awar cewa tana kokarin ganin an kawo karshen yaki a kan kasar Yemen, inda al'ummar kasar ta Yemen ke kallon hakan a matsayin yaudara irin da wadda gwamnatin da ta gabata a kasar ta Amurka ta rika yi kan batun yakin Yemen.