IQNA

An Bude Babban Baje Kolin Littafai Na Duniya A Birnin Alkahira Na Kasar Masar

22:30 - July 04, 2021
Lambar Labari: 3486076
Tehran (IQNA) an bude babban baje kolin littafai na kasa da kasa karo na 52 a birnin Alkahira na kasar Masar.

Jaridar Alahram ta bayar da rahoton cewa, an bude babban baje kolin littafai na kasa da kasa karo na 52 a birnin Alkahira na kasar Masar, tare da halartar daruruwan madaba'antu na ciki da wajen kasar.

Cibiyoyin ilimi daban-daban na kasar Masar suna nuna littafai da suka samar a bangarori daban-daban na ilimi, da hakan ya hada da ilmomi na addini da kuma ilmomi na zamani.

Baya ga haka kuma da dama daga cikin madaba'antu na kasar suna gabatar da littafan da suka buga, musamman ma sabbi daga cikinsu.

Kamar yadda kuma madaba'antu da kamfanonin buga littafai na kasashen duniya suna halartar wannan babban baje koli domin nuna irin littafan da suka samar.

Cibiyar Azhar na daga cikin cibiyoyin da suke nuna littafansu a wannan baje kolin tun daga lokacin da aka fara shi shekaru hamsin da biyu da suka gabata, inda take nuna littfai da manyan malaman cibiyar gami da na dalibai da suka kammala karatu a fagage daban-daba na ilimi.

Baje kolin littfana na kasa da kasa zai ci gaba da gudana a birnin Alkahira har zuwa ranar 15 ga wannan wata na Yuli da muke ciki.

 

 

 

3981720

 

 

captcha