IQNA

Sabon Firayi Ministan Gwamnatin Isra'ila Ya Fuskanci Turjiya A Majalisa

21:24 - July 06, 2021
Lambar Labari: 3486080
Tehran (IQNA) sabon firayi ministan gwamnatin yahudawan Isra'ila ya fara da fuskantar turjiya a majalisar dokoki.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, sabuwar gwamnatin yahudawan Isra'ila ta fara karawa da 'yan adawa a majalisar Knesset, bayan da ta kasa sabunta dokar bai wa Falastinawa  hakkin zama dan kasa.

A zaman da majalisar dokokin Isra'ila ta Knesset ta gudanar a daren jiya na tsawon sa'oi, an kada kuri'a kan batun sabunta dokar da ta bayar da dama ga Falastinawa masu iyali a cikin yankunan da Isra'ila ta mamaye hakkin zama dan kasa.

Daga karshe dai wadanda suka amince da kuma wadanda ba su amince ba adadinsu ya zo daidai, saboda haka an tashi ba tare da amincewa kan sabunta dokar ba.

'Yan adawa karkashin jagorancin tsohon Firayi ministan gwamnatin yahudawan Benjamin Netanyahu ne suka kawo ma sabuwar gwamnatin cikas kan wannan batu.

A tsawon shekarun da Netayahu ya yi a kan kujerar shugaban gwamnatin Isra'ila, 'yan majalisar daga bangaren jam'iyyarsa ta Likud suna kada kuri'ar amincewa da sabunta wannan doka a kowace shekara, amma a wannan karon suka yi fatali da ita.

 

3982302

 

Abubuwan Da Ya Shafa: falastinawa
captcha