IQNA

Nuna Kwafin Linjila Da Kur'ani Na Tarihi A Cikin Ginin Cibiyar ISESCO

22:08 - July 12, 2021
Lambar Labari: 3486098
Tehran (IQNA) an nuna kwafin littafan Linjila da kur'ani na tarihi a cikin ginin cibiyar ISESCO.

Cibiyar yada ilimi da al'adun musulunci ta kasashen musulmi wato ISESCO ta sanar da cewa, a gininta da ke birnin Rabat na kasar Morocco, ana gudanar da baje kolin nuna dadaddun littafai da suka hada kwafin kur'ani da kuma Linjila.

Bayanin ya ce a wurin wannan baje koli ana nuna wani kur'ani da aka rubuta shi tun fiye da shekaru dubu daya da suka gabata, kamar yadda kuma akwai tsohon kwafi na littafin Linjila.

Baya ga haka kuma akwai tsoffin littafai da aka buga tun daruruwan shekaru masu yawa wadanda wannan cibiya ta samu.

Wannan cibiya dai tana gudanar da ayyukanta ne a dukkanin kasashen msuulmi, inda take bayar da muhimmanci ga ayyuka na bunkasa ilimi, da kuma sauran abubuwa na tarihin musulunci, domin tabbatar da cewa sun wanzu.

3983461

 

captcha