IQNA

An Shiga Wata Sabuwar Dambarwar Siyasa A Kasar Tunisia

16:07 - July 26, 2021
Lambar Labari: 3486140
Tehran (IQNA) bayan sanar da tunbuke firayi minista da kuma shugaban majalisar dokoki An shiga wani wani hali na rashin tabbas a kasar Tunisia,

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, tun daga lokacin da shugaban kasar Tunisia Qais Saeed ya sanar da dakatar da majalisar ministocin kasa da kuma sauke shugaban majalisar dokoki, kasar ta shiga wata sabuwar danbarwa ta siyasa.

Shugaban kasar Tunisia Qais Saeed ya bayyana cewa, ya dauki wannan matakin ne saboda maslahar kasar, da kuma kokarin ganin an ceto ta daga durkushewa, bayan kasawar gwamnatin Firaministan Hesham Mechichi, wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a kanta wanda al’ummar kasar ke jiran gani daga gare ta.

Daya daga cikin dalilan shi ne kasa shawo kan matsalar cutar corona, ko kuma daukar matakan da suka dace domin dakile matsalar, wadda take lakume rayukan jama’a a kasar.

Baya ga haka kuma shugaban na Tunisia ya bayyana majalisar dokokin kasar da cewa, tana aiwatar da manufofin jam’iyyu e kawai, musamman ma wadanda suka yi babakere a cikin majalisar, maimakon yin aiki da jama’a suke bukata.

Sai dai mataki na shugaban Tunisia ya fuskanci kakkausan martani daga wasu jam’iyyun kasar, musamman jam’iyyar Nahda, yayin da kuma a daya bangaren jama'ar gari da dama suka bayyana gamsuwarsu da wannan mataki.

 

3986434

 

captcha