IQNA

Ana Kayata Hubbaren Imam Ali (AS) Kafin Ranar Idin Ghadir

22:27 - July 26, 2021
Lambar Labari: 3486142
Tehran (IQNA) a daidai lokacin da ya rage 'yan kwanaki a gudanar da tarukan idin Ghadir, an fara kayata hubbaren Imam Ali Ali (AS).

An fara kayata hubbaren Imam Ali Ali (AS) da ke burnin najaf a kasar Iraki, a daidai lokacin da ya rage 'yan kwanaki a gudanar da tarukan idin Ghadir.

A kowace shekara dai mabiya tafarkin Ahlul bait (AS) sukan gudanar da taruka a hubbaren Imam Ali (AS) da yake birnin Najaf Asharaf, kamar yadda kuma akan gudanar da irin wadanna taruka a sauran hubbarori na limaman ahlul bait amincin Allah ya tabbata a gare su.

Ranar Ghadir dai tana a matsayin cikar addini, wadda a ranar manzon Allah (SAW) ya yi huduba ta karshe bayan kammala aikin hajjin bankwana.

A wanann ranar ce manzon Allah (SAW) ya fayyace makomar lamaurra a bayansa, tare da baiwa al'umma mafita matukar dai ta yi riko da wasiyarsa, wanda kuma wannan rana tana a matsayin kammalar addinin Allah.

3986440

 

captcha