IQNA

Yariya Mai Larurar Gani Wadda Ta Hardace Kur'ani Tun Tana Da Shekaru 7

23:28 - August 02, 2021
Lambar Labari: 3486163
Tehran (IQNA) yarinya mai larurar gani wadda ta hardace kur'ani mai tsarki tun tana da shekaru 7 da haihuwa.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, Hunain Ashraf Abulainain Muhammad yarinya ce mai larurar gani wadda ta hardace kur'ani mai tsarki tun tana da shekaru 7 da haihuwa a kasar Masar.

Tun bayan haihuwarta da 'yan watanni ne Hunain ta samu matsalar ciwon daji, wanda ya yi sanadiyyar har ta rasa idanunta tana da watanni 9 a duniya, amma da taimakon Allah ta samu sauki.

Tun tana karama mahaifanta suke koyar da ita karatun kur'ani, a lokacin da ta kai shekaru 7 da haihuwa ta kamala hardar kur'ani mai tsarki baki daya.

Baya ga haka kuma ta shiga gasar karatun kur'ani mai tsarki sau 20, kuma a kowace gasar ita ce take zuwa ta daya a bangaren hardar kur'ani mai tsarki.

 

3987821

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: haihuwa ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha