IQNA

An Bude Bangaren Harshe Na 20 Daga Cikin Harsunan Da IQNA Ke Watsa Labarai Da Su

17:29 - August 11, 2021
Lambar Labari: 3486190
Tehran (IQNA) an kara harshen Malayo a cikin harsunan da kamfanin dillancin labaran iqna yake watsa labaransa.

An gudanar da bikin kara harshen Malayo a matsayin harshe na ashirin daga harsunan da kamfanin dillancin labaran iqna yake watsa labaransa da su a duniya.

Taron ya samu halartar babban jami'i mai kula da kamfanonin dillancin labarai na kasar Iran Sayyid Saeed Redha Amuli, da kuma Sayyid Hamid Redha Tayyibi shugaban bangaren yada labarai na jami'oin kasa, sai kuma manajan darakta na kamfanin dillancin labaran iqna Mohammad Hussain Hasani.

Harshen malayo dai yana daga cikin amnyan harsuna masu matukar muhimamnci a duniya, kasantuwar cewa harshe ne da daruruwan miliyoyin mutane suke yin magana da shi a gabashin nahiyar Asia.

Daga cikin kasashen da suke yin magana da wannan harshe a hukuamnce akwai Indonesia, sai kuma kasar malaysia, hakan nan kuma wasu daga cikin kasashen yankin kamar Philippens da kuma Singapore duk suna magana da shi.

Baya ga haka kuma an gudanar da ayyuka masu matukar muhimmanci na addinin muslucni da wannan harshe, baya ga tarjamomin na kur'ani mai tsarki, an kuma yi rubuce-rubuce na littafai da dama a bangarori daban-daban na addinin muslunci a  cikin  wannan harshe, wanda masu fahimtarsa suke amfana da su.

 

3988371

 

 

 

 

 

captcha