IQNA

Ana Shirye-Shiryen Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Mata Ta Duniya A UAE

20:08 - August 22, 2021
Lambar Labari: 3486226
Tehran (IQNA) an fara rijistar sunayen mata masu shawar shiga gasar kur'ani ta duniya ta mata a UAE.

Shafin yada labarai na Albayan ya bayar da rahoton cewa, Ibrahim Muhammad Bumalha babban mai bayar da shawara ga sarkin Dubai kan harkokin addini ya sanar da cewa an fara rijistar sunayen mata masu shawar shiga gasar kur'ani ta duniya ta mata a kasar Hadaddiyar daular Larabawa, wadda ake yi wa taken gasar kur'ani ta Shaikha Fatima Bint Mubarak.

Ya ce sakamakon matsaloli na kiwon lafiya musamman cutar corona da ta addabi duniya, wannan ne yasa aka aka jinkirta gudanar da gasar.

Dangane da gasar a bangaren maza ya ce an samu damar gudanar da ita a cikin watan ramadan da ya gaba cikin nasara.

Za a kammala rijistar sunayen wadanda suke son shiga gasar daga nan zuwa 15 ga watan Satumba mai kamawa, sannan za su iya ziyartar shafin yanar gizo na: info@quran.gov.ae یا quran@eim.ae 

Sannan kuma ya bayyana sharudda na gudanar da gasar a bangaren mata wadda za a gudanar a nan gaba, inda ya ce mata da suke bukatar shiga gasar dole ne su kasance mahardata kur'ani da kuma sanain hukunce-hukunce na karatun kur'ani wato tajwidi, sannan shekarunsa kada su wuce 25 da haihuwa. 

 

3992196

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hadaddiyar daular larabawa ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :