IQNA

Bayan Kwashe Shekaru 27 An Janye Dokar Hana Saka Hijabi A Makarantu A Kasar Uzbekistan

22:13 - September 08, 2021
Lambar Labari: 3486287
Tehran (IQNA) bayan kwashe tsawon shekaru 27 an janye dokar hana saka hijabi ga mata a cikin makarantu a kasar uzbekistan

Tashar TRT Arabic ta bayar da rahoton, a  wani mataki na bazata, ayan kwashe tsawon shekaru 27 an janye dokar hana saka hijabi ga mata a cikin makarantu a kasar uzbekistan.

Wannan na zuwa nea  cikin wata sanarwa da minista ilimi na kasar Shirzad Shirmanuv ya fitar nea  yau, inda ya ce an janye dokar wadda ta dauki tsawon shekaru ana aiki da ita.

Ya ce matakin na zuwa ne a kokarin gwamnati na kara bayar da dama ga mutane su yi addininsu a cikin 'yanci ba tare da takurawa ko shiga hakkinsu ba.

Sai dai da dama daga cikin masana da kuma masu bin diddigin lamurra suna ganin cewa matakin ya zo ne sakamakon sauyin da aka samu a kasar afghanistan, bayan da Taliban ta kwace iko da kasar.

Inda suke ganin cewa, gwamnatin Uzbekistan ta dauki matakin ne domin rage tayar da jijiyoyin wuya kan lamurran a suka shafi addini, domin kada ta jawo ma kanta matsala, musamman ganin cewa Taliban na makwabtaka da ita.

Tun lokacin mulkin tarayyar Soviet ne dai ake daukar matakan takura ma mutane a kasar uzbekistan kan lamurra da suka shafi addini.

 

captcha