IQNA

Farin Jinin Joe Biden Ya ragu Matuka A Amurka Bayan Janyewa Daga Afghanistan

21:22 - September 12, 2021
Lambar Labari: 3486300
Tehran (IQNA) Farfesa Richard Bensel ya bayyana cewa, farin jinin da Joe Biden yake da shi tsakanin Amurkawa ya ragu matuka bayan janyewa daga Afghanistan.

A zantawarasa da kamfanin dillancin labaran iqna, Farfesa Richard Bensel malami a jami'ar Cornell da ke kasar Amurka ya bayyana cewa, farin jinin da Joe Biden yake da shi tsakanin Amurkawa ya ragu matuka bayan janyewa daga Afghanistan.

Ya ce matakin janyewar Amurka daga kasar Afghanistan da kuma yadda aka aiwatar da hakan cikin kankanin lokaci ya baiawa kowa mamaki a Amurka, duk da cewa Biden ya danganta hakan da matsaloli na tattalin arziki da kuma asarorin da hakan ke jawowa Amurka.

Farfesa Bensel ya ce, abin da yafi dangane da janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan shi ne, yadda suka janye ba tare da sun yi wani shiri na taimaka ma kasar ba domin ta tsaya a kan kafafunta, ta fuskoki na tsaro da tattalin arziki da kuma kyautata rayuwar jama'ar kasar, domin kasantuwar Amurka yasa kasar a cikin manyan kalubale a dukkanin wadannan fuskoki.

 

3996030

 

 

captcha