IQNA

An Fara Gudanar Da Bincike Kan Kona Wani Masallaci A Birnin Manchester

21:53 - September 12, 2021
Lambar Labari: 3486301
Tehran (IQNA) an fara gudanar da bincike kan cinna wuta da wasu suka yi a wani masalaci da ke birnin Manchester na kasar Burtaniya.

Jaridar Guardian ta kasar Burtaniya ta bayar da rahoton cewa, 'yan sanda sun shiga gudanar da bincike kan sanya wuta da aka yi a kan wani masallaci na musulmi a daren jiya Asabar a garin Manchester.

Rahoton ya ce an sanya wutar ne da dare bayan da musulmi da suke gudanar da harkokinsu a wurin suka bar wurin, inda aka saka wuta da ta yi sanadin jawo gobara a masallacin.

Kafin zuwan jami'an kwana-kwana, wasu daga cikin jama'ar gari da suke wucewa sun fara kawo dauki domin kashe wutar da ke ci a masallacin.

Musulmin da suke tafiyar da lamurran masallacin sun yi godiya ga jama'ar yankin, kan yadda suka nuna damuwa da abin da ya faru da kuma gudunmawar da suka bayar wajen kashe wutar da ke ci a  masallacin, lamarin da a cewarsu ya nuna musulmi da al'ummar yankin suna zaune laffiya ne da girmama juna.

A nasu bangaren 'yan sanda a birnin na Manchester suna ganin cewa harin yana da alaka ne da wasu masu akidar kiyayya da addinin muslunci, kuma sun sha alwashin bin kadun lamarin domin gano wadanda suke da hannu a cikin lamarin domin su gurfana a gaban kuliya.

 

3996959

 

captcha