IQNA

Allah Ya Yi Makarancin Kur'ani Matashi Dan Kasar Masar Rasuwa Sakamakon Bugun Zuciya

23:23 - September 15, 2021
Lambar Labari: 3486314
Tehran (IQNA) Mahmud Abdulsattar al-Atwi makarancin kur'ani kuma mahardaci ya rasu bayan samun matsalar bugun zuciya a jiya.

Shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, a jiya Allah ya yi wa Mahmud Abdulsattar al-Atwi makarancin kur'ani kuma mahardaci rasuwa bayan samun matsalar bugun zuciya a kauyen Shabanat da ke lardin Shaqiyyah a kasar Masar, wanda ya rasu yana da shekaru 26 a duniya.

Muhammad Abdulsattar mahaifin Mahmud Abdulsattar ya bayyana cewa, dansa yana daga cikin matasa masu tarbiya ta addini da kuma riko da kur'ani mai tsarki a cikin rayuwarsa.

Ya ce dansa ya kasance tun daga lokacin kuruciyarsa, yaro ne mai son addini mai riko da kyawawan dabi'u da girmama na gaba, da kuma son zama da malamai.

Da farko dai ya fara da koyon tilawa, inda ya shahara a kauyensu da kyakyawan sautinsa na karatun kur'ani, daga bisani kuma ya shiga harda kur'ani inda ya kammala harda a cikin kankanin lokaci.

قاری جوان مصری درگذشت + فیلم تلاوت

 

 
 

3997655

 

Abubuwan Da Ya Shafa: bugun zuciya mahardaci matasa son addini
captcha