IQNA

An Fara Gudanar Da Tarukan Arba'in A Hubbaren Sayyida Zainab A Birnin Damuscus Na Syria

17:40 - September 19, 2021
Lambar Labari: 3486326
Tehran (IQNA) an fara gudanar da tarukan arba'in na Imam Hussain (AS) a hubbaren Sayyida Zainab da ke birnin Damascus na kasar Syria.

Rahotani daga kasar Syria na cewa, an fara gudanar da tarukan arba'in na Imam Hussain (AS) a hubbaren Sayyida Zainab da ke kudancin birnin Damascus fadar mulkin kasar.

Wadannan taruka za su ci gaba da gudana har zuwa ranar arba'in na Imam Hussain (AS), inda malamai suke gabatar da jawabai kan abin da ya faru da zuriyar manzon Allah (SAW) karkashin jagorancin Imam Hussain (AS) a hannun sarakunan daular Bani Umayya, na cin zarafi da kisan gilla da tozarci.

 

3998506

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha