IQNA

Irakawa Sun Bayyana Yunkurin Kurdawan Kasar Na Neman Kulla Alaka Da Isra'ila Da Cewa Ha'inci Ne

22:50 - September 25, 2021
Lambar Labari: 3486349
Tehran (IQNA) Irakawa sun nuna bacin ransu kan yunkurin kulla alaka da Isra'ila da Kurdawan kasar ke shirin yi.

Kamfanin dillancin labaran Mawazin News ya bayar da rahoton cewa, kungiyoyi da jam'yyun siyasa na Irakawa sun nuna bacin ransu kan yunkurin kulla alaka da Isra'ila da Kurdawan kasar ke shirin yi.

Kungiyoyi da fitattuna mutane a kasar Iraki sun yi allawadai da taron Arbil, inda wasu Irakawa kimani 300 suka gudanar da taro a wani hotel babban birnin yankin Kurdiwa ta kasar, inda masu jawabi a taron suka yi ta kira ga gwamnatin kasar ta shiga cikin abinda suke kira ‘yarjejeniyar Ibrahimiyya’.

Wata kungiya wacce ake kira “Peace Communicatioon’ wacce kuma take da mazauni a birnin NewYork na kasar Amurka ce ta shirya taron na Arbil a jiya jumma’a.

Amma kungiyoyin ‘farkawa’ ko (Assahwah) na kasar Iraki da dama sun yi allawadai da taron sun kuma kara jadadda matsayinsu na goyon baya ga al-ummar Falasdinu a gwagwarmaya da suke da Isra’ila, inji Ahmed Abu Risha mai magana da yawun kungiyoyin.

Kafin haka dai shugaban kasar Iraki Barham Saleh ya yi watsi da duk wani kokari na samar da hulda da Isar’ila. Don mutanen kasar Iraki basa son hakan, suna kuma goyon bayan al-ummar Falasdinu.

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ne ya samar da abin da ya kira ‘yarjejeniyar Ibrahimmiya’ inda a bisa hakan ne wasu daga cikin kasashen larabawa suka kulla hulda da gwamnatin yahudawan Isra'ila.

 

4000154

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kurdawa ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha